Wasu yan bindiga sun kashe, Ahmad Areeda,dan kasuwa mutumin kasar Siriya, mazaunin Kano kafin su yi garkuwa da dansa mai shekaru 14.
Lamarin ya faru ne a daren ranar Talata a kan titin asibitin Muhammadu Abdullahi Wase a unguwar Nassarawa dake cikin birnin Kano.
Yan bindigar sun harbe marigayin bayan da ya nuna tirjiya lokacin da suka yi kokarin yin garkuwa da dansa mai suna, Muhammad Ahmed.
A cewar wasu da suka ganewa idonsu abin da ya faru sun ce yan bindigar sun kai su 8.
Wani sheda da yaki yarda ya bayyana sunansa ya ce,”Ya rufe shagonsa wajen karfe 8 inda ya je daukar motarsa a ofishin hukumar bada agaji ta Red Cross inda ya saba ajiye motarsa ashe tuni yan bindigar na jiransa a bakin ofishin cikin wata koriyar mota kirar Peugeot wacce aka rufe gilashinta da bakin abu wasu daga cikinsu sun bi marigayin zuwa cikin harabar wasu kuma suka tsaya a waje cikin motar.
“Wadanda suka bi mutumin dan kasar Siriya su ne suka harbe shi aka kama suka dauke dansa.”
Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, Magaji Musa Majiya ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce tuni rundunar ta fara bincike kan lamarin.