Yan Bindiga Sun Kashe Wani Ma’aikaci Dan Kasar Waje Da Kuma Wasu Mutane Biyu A Jihar Kogi 


Hoto:Daily Trust

Wasu yan bindiga da ake zargin cewa masu satar mutane ne sun kashe wani maaikaci dan kasar waje da kuma wasu mutane biyu akan babbar  hanyar Lokoja zuwa Ajaokuta a jihar Kogi. 

Jaridar Daily Trust ta gano cewa ma’aikacin dan kasar waje na tafiya ne tare da dan sandan dake masa rakiya  da kuma wani ma’aikaci lokacin da suka ci karo da yan bindigar. 

Kokarin da jami’in dan sandan yayi na hana yin garkuwa da mutumin ne ya jawo musayar wutar da takai ga mutuwar dan sandan, da kwararren ma’aikacin dan kasar waje da kuma daya ma’aikacin. 

 Bata garin dai sunji haushin abinda dan sandan dake rakiyar ma’aikacin  yayi musu wanda har takai ga musayar wutar.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Kogi, William Aya,wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, yace rundunar ta fara bincike domin gano wadanda suka aikata wannan danyen aikin. 

You may also like