‘Yan Bindiga Sun Kashe Wasu Mutane Ta Hanyar Banka Masu Wuta A RamiHukumomi a Nigeria sun bayar da tabbacin kubutar da wasu ‘yan kasar China su 7 da ‘yan bindiga su ka yi garkuwa da su a jihar Neja.

Tun a cikin watan Yunin da ya gabata ne dai ‘yan bindigar suka aukawa ‘yan kasar Chinan a wani wurin hakar ma’adanan karkashin kasa da ke yankin Shiroro, mai fama da ‘yan bindiga da hukumomin jihar su ka ce mayakan kungiyar Boko Haram ne.

Yan Kasar China Da Sojojin Najeriya suka ceto bayan anyi garkuwa da su

Yan Kasar China Da Sojojin Najeriya suka ceto bayan anyi garkuwa da su

A cikin hirar shi da Muryar Amurka, Mr. Emmanuel Umar kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Nejan, yace an samu nasarar kubutar da ‘yan Chinan ne a sakamakon hare haren da gamayyar jami’an tsaron Nigeria suka kai wa ‘yan ta’addan a maboyarsu.

Sai dai a yayin da aka samu Nasarar kwato wadannan ‘yan China, rahotanni daga yankin na Shiroro na nuna cewa, ‘yan bindigar sun hallaka wasu mutanen 7 ta hanyar tura su rami sannan suka banka masu wuta a ranar Asabar din nan ta karshen mako.

Yan Kasar China Da Sojojin Najeriya suka ceto bayan anyi garkuwa da su

Yan Kasar China Da Sojojin Najeriya suka ceto bayan anyi garkuwa da su

Kawo lokacin hada wannan rahoto dai babu wani karin haske daga rundunar ‘yan sanda ta jihar Neja akan wannan sabon hari.

Kwamishin tsaron cikin gida na jihar Emmanuel Umar yace gwamnati na kokarin kawar da wadannan mahara da suka addabi jama’a.

Saurari rahoton cikin sauti:Source link


Like it? Share with your friends!

-1

You may also like