Yan sanda biyu sun rasa rayukansu,bayan da wasu mutane suka harbesu a kan titin Mongogo -Okene dake jihar Kogi.
Maharan sun kuma yi awon gaba da bindigogin yan sandan kirar AK-47.
Kwamishinan yansandan jihar Mista Wilson Inalegwu ya tabbatar da mutuwar yan sandan.
Inalegwu wanda ya bayyana kisan a matsayin wani abin bakin ciki,yace za abi sawun maharan da suka tsere domin kama su.
Mai rikon mukamin Shugabancin karamar hukumar Ogori-Mangogo wacce a cikinta aka kashe mutanen,Mista Moses Akande yayi Allah wadai da kisan inda ya bayyana shi a matsayin wani abu da bai dace ba.
Yayi fatan yan sanda zasu kama wadanda sukayi kisan domin su fuskanci Shari’a.