Yan bindiga sun kashe yan sanda uku kana suka yi garkuwa da wani dan kasar Syria a jihar Sokoto


Rundunar yan sandan jihar Sokoto ta tabbatar da kisan yan sanda uku da kuma yin garkuwa da Abu Nasir, wani dan kasar Syria da ke aiki a wani kamfanin gine-gine a jihar.

Cordelia Nwawe, mai magana da yawun rundunar ta ce lamarin yafaru ne da misalin karfe 7:20 na safiyar ranar Laraba.

Maharan sun dirarwa wurin hakar dutse na kamfanin Triacta dake kauyen Lambar Mazaru a karamar hukumar Bodinga dake jihar.

Nwawe ta ce an tabbatar da mutuwar yan sanda uku dake gadin wurin asibiti ya yin da ba’a san inda aka kai ma’aikacin kamfanin ba.

Ta ce tuni yan sanda suka fara bincike don ganin an ceto dan kasar ta syria da kuma hukunta wadanda suka aikata haka.

Yayin da wakilin Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya ziyarci wurin da lamarin ya faru wasu gadi da ke gadin wurin haka da farfasa duwatsun sun ce wasu bata gari hudu ne dake cikin wata mota mai bakin gilashi su ne suka kai hari wurin.

Suka ce yan bindigar suna zuwa suka bude wuta akan yan sandan ba tare da bata lokaci ba.

You may also like