Yan bindiga sun sace wani basaraken gargajiya a jihar Rivers


Yan bindiga sun sace, Eze, G.A.O Omodu basaraken gargajiya na  Mgobuolua dake al’ummar Rundele a ƙaramar hukumar Emohua ta jihar Rivers.

Bata garin sun sace basaraken gargajiyar daga gidansa da  sassafe inda suka yi gaba da shi a cikin motarsa.

Wata majiya dake da kusanci da iyalinsa ta shedawa manema labarai  cewa an gano motar basaraken a yankin Rumuji-Ndele dake kan titin East-West.

Tuni matasan yankin suka shiga dajukan dake yankin domin neman basaraekn har yanzu masu garkuwar basu tuntubi iyalinsa ba.

Mai magana da yawun rundunar yan sanda ta jihar DSP Nnamdi Omoni ya ce tuni aka tura jami’an tsaro zuwa yankin don ganin an samu nasarar ceto basaraken.

Garkuwa da mutane a Najeriya, musamman ma a yankin kudu maso gabashin ƙasar abune  da ya zama ruwan dare kuma yake nema ya gagari jami’an tsaro.

You may also like