Yan bindiga sun sace wani dan majalisar dokokin jihar Taraba


Hoton wasu da suka sace wani yaro a Kano

Rundunar yan’sanda jihar Taraba, a ranar Lahadi ta tabbatar da sace dan majalisar dokokin jihar, Hosea Ibi da wasu yan bindiga uku waɗanda ba a san ko su waye ba suka yi.

Ibi na wakiltar mazabar Takum 1 a majalisar dokokin jihar.

David Misal, mai magana da yawun rundunar ya ce ya ce an yi garkuwa da Ibi a Takum mahaifarsa ranar Lahadi da daddare.

 “Zan iya tabbatar maka cewa an yi garkuwa da dan majalisar da daren jiya a Takum.Iya abinda zan iya fada maka kenan a yanzu,”Misal ya ce.

Mai magana da yawun rundunar yace tuni suka tura ƙarin jami’ai zuwa Takum domin ceto dan majalisar.

Rimansikpe Tsokwa, wani sheda da yaga yadda aka sace ɗan majalisar ya fadawa kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN cewa an sace Ibi wajen karfe 10 na dare.

“Yan bindiga su uku suka sauko daga kan babur da misalin karfe 10 inda suka shiga gidan babar Hosea,” yace.

You may also like