Yan bindiga sun sace ya’yan dan majalisa su 2 tare da kashe wasu kauyawa 3 a Zamfara


Yan’sanda a jihar Zamfara sun tabbatar da sace  wasu mutane biyu ya’yan Yahaya Chado,  ɗan majalisar wakilai ta tarayya maiwakiltar mazabar Maradun/Bakura.

Mai magana da yawun rundunar yan’sandan jihar, Muhammad Shehu ya fadawa yan jaridu a Gusau ranar Litinin cewa anyi garkuwa da ya’yan dan majalisar ne bayan da wasu yan bindiga suka dirarwa gidansa dake ƙauyen Gora a Ƙaramar Hukumar Maradun.

Ya ce mutane uku aka kashe, huɗu kuma suka jikkata a harin da aka kai da karfe 1 na daren ranar Litinin.

Daya  daga cikin mazauna ƙauyen, Kabiru Mai-kwashe, ya fadawa  Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN cewa masu garkuwar sun zo akan babura 20 inda kowanne babur ke ɗauke da mutane biyu riƙe da makamai.

“Sun yi harbin iska ba ƙaƙƙautawa kafin su shiga gidan da suka zo.

“Yan bindigar ta karfin tuwo  suka tafi da mutanen biyu, Muhammad Yahaya mai shekaru  27 da kuma yayansa Junaid Yahaya wanda ya kusa kaiwa shekara 35,” ya ce.

A cewarsa bayan da yan bindigar suka bar gidan sun kuma harbe mutane uku har lahira tare da jikkata wasu huɗu. 

Mai-Kwashe ya ƙara da cewa ɗaya daga cikin mutanen da aka sace ya dawo gida riƙe da nambar tarho inda suke umarta mahaifinsa ya kira su “idan yana son sake gani babban dansa.”

NAN ya gano cewa masu garkuwa sun bukaci kuɗin fansa miliyan 10 kafin su sako wanda suke garkuwa da shi.

You may also like