
Yan bindiga sun sake yin garkuwa da dattijo dan shekara 74 mai suna Atser Kyausu, mahaifin fitaccen dan kasuwar nan, Cif Athansius Kyausu a jihar Benue daga gidansa dake karamar hukumar Vandeikiya ta jihar.
Tun farko dattijon an taba yin garkuwa da shi a cikin watan Yuli na shekarar 2015 da wasu yan bindiga suka yi waɗanda suka amince da cewa sun aikata laifin ne bayan da wani kafinta da mutumin ya kira ya gyara masa rufin gida ya basu bayanai akansa.
Sai dai a wancan lokacin yan sanda sun samu nasarar ceto Kyausu bayan da suka yi musayar wuta da masu garkuwar a wani ƙauye dake jihar.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar,Moses Joel Yamu ya ce sace Atser da akayi a wannan karon ranar 28 ga watan Disambar 2017 wasu yan bindiga ne da suka je gidansa cikin wata mota ƙirar Toyota da misalin karfe 8 na dare suka yi.
Yamu ya kara da cewa yan bindigar sun cusa tsohon cikin motar kafin inda suka yi gaba kuma tun daga wannan lokaci ba a sake jin duriyarsa ba.