Yan bindiga sun yi garkuwa da sakataren kudi na jam’iyyar PDP a jihar Ekiti


Wasu yan bindiga da ba a san ko suwaye ba sunyi garkuwa da sakataren kudi na jam’iyyar PDP reshen jihar Ekiti, Kayode Oni.

An yi garkuwa da Oni akan babbar hanyar Efon Alaaye-Erio-Ekiti a hanyarsa ta komawa gida dake Arakomo Ekiti, hedikwatar karamar hukumar Ekiti ta yamma.

Jackson Adebayo, sakataren yada labaran jam’iyar wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce Oni yaje gudanar da zaben shugabannin jam’iyar PDP a matakin karamar hukuma inda aka yi garkuwa da shi akan hanyarsa ta dawowa.

Adebayo ya ce tuni masu garkuwar suka tuntubi matarsa da kuma dan uwansa inda suke neman a biya su miliyan ₦30 a matsayin kudin fansa kafin su sako shi.

Abdullahi Chafe, kwamishinan yan sandan jihar ya ce zai bukaci lokaci kafin ya yi magana akan batun saboda ya yi tafiya ya zuwa wajen jihar amma zai koma nan ba da dadewa.

Garkuwar da aka yi da Oni na zuwa ne yan watanni da yin garkuwa da wani jigo a jam’iyar APC ta jihar,Ayo Arise, wanda tsohon sanata ne.

Arise ya samu yanci ne bayan da aka biya kudin fansa.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like