Yan bindiga sun yi garkuwa da sakataren SUBEB  a Kano


Wasu masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da, Alhaji Uba Muhammad Shiye,sakataren Hukumar Ilimin Bai Daya ta Jihar Kano (SUBEB).

Wasu yan bindiga ne da ba a san ko su waye ba su ka yi garkuwa da Shiye a gidansa dake Shiye Karamar Hukumar Bunkure ta jihar.

Dan uwansa wanda ya nemi a boye sunansa ya ce mutanen da su ka yi garkuwa da shi sun nemi a basu kudin fansa miliyan ₦20.

“Masu garkuwa da dan uwana sun kira iyalinsa ta waya inda suka nemi a basu kudin fansa miliyan ₦20. Sun yi alkawarin da zarar mun ba su kudin.

“Ina kira ga wadanda su ka yi garkuwa da dan uwa na da su duba halin da muke ciki dan ginmu ba masu kudi ba ne bamu da kudin da suke bukata saboda haka nake rokonsu da su saki dan uwana saboda Allah.”

Da yake tabbatar da faruwar lamarin mai magana da yawun rundunar yan sandan ta jihar Kano, Magaji Musa Majiya, ya ce an yi garkuwa da sakataren a gidansa da ke kauyen  Shiye.

Majia ya kara da cewa tuni kwamishinan yan sandan jihar, Rabi’u Yusuf, ya tura runduna ta musamman dake yaki da fashi da makami, SARS zuwa karamar hukumar Bunkure domin su binciko sakataren da aka yi garkuwa da shi.

You may also like