‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Wani Tsohon Minista



Rundunar ‘yan sandan jihar Nassarawa ta tabbatar da yin garkuwa da tsohon ministan kwadago, Mista Husaaini Akwanga.

Mista Akwanga ya yi ministan ne a zamanin mulkin Obasanjo amma daga bisani an tsige shi a ranar 4 ga Disamba, 2003 sakamakon badakalar dala milyan 214 na kudin katin shedar dan kasa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa, DSP Kennedy Idirisu wanda ya tabbatar da hakan a yau Laraba, ya ce ‘yan bindigan sun yi garkuwa da tsohon ministan ne a jiya Talata a gonarsa dake kan titin Wamba a garin Akwanga.

Kusan nisan kilomita 46 ne ke tsakanin Akwanga da babban birnin jihar Nassarawa wato Lafia.

DSP Idirisu ya kara da cewa yanzu haka kwamishinan ‘yan sandan jihar Abubakar Sadiq Bello ya nada runduna karkashin jagorancin mataimakin kwamishinan ‘yan sandan domin bankado wadanda suka yi garkuwa da Mista Akwanga.

A gefe daya kuma, wata majiya daga iyalan tsohon ministan ta tabbatar da cewa masu garkuwar sun yi magana da su inda suke bukatar makuden kudade kafin su sake shi.

Idan za a iya tunawa, a ranar 6 ga Mayu na wannan shekarar, an yi garkuwa da mahaifiya da ‘yar uwar dan majalisar jihar Nassarawa, Honarabul Kassim Mohammed a garin na Akwanga.

You may also like