‘Yan bindigan Kwango sun kashe mutane 10


 

Akalla mutane 10 sun mutu yayin wani artabu tsakanin ‘yan bindiga da sojoji a wani mummunan hari da ake zargin ‘yan tawayen Yuganda da kaiwa a gabashin Kwango.

Kämpfe im Ostkongo (Phil Moore/AFP/Getty Images)

Wadanda suka shaidar da aukuwar lamarin sun bayana cewa a karshen mako ne maharan dauke da manyan makamai sun yi artabu da sojoji a garin Beni da ke gabashin Kwango.

Garin na Beni dai ya sha fama da hare-haren ‘yan tada kayar baya sama da shekaru goma. Sai dai kakakin rundunar ‘yansanda da ke ayyukan sintiri a yankin, ya ce ba bu cikakkun bayanai akan hakikanin adadin mutanen da suka mutu a harin amma mazauna yankin na na ci gaba da jigilar fidda gawargaki da ake zaton na mayakan ne da sojojin suka kashe.

Ko da yake wasu rahotanni na cewa mayakan sun hallaka sojoji biyu hade da fararen hula takwas a harin, Majalisar Dinkin Duniya ta ce tun a shakarar 2014, gabashin Kwango ke fama da matsalar rashin tasaro, inda bayanai ke cewa mutane 700 ne ‘yan ta’addan suka kashe a kusa da garin na Beni.

 


Like it? Share with your friends!

0

You may also like