Yan Boko Haram Na Taruwa A Dajin Suntai Dake Jihar Taraba Bayan Sun Tsere Daga Sambisa Yan kungiyar Boko Haram da suke tserewa daga dajin Sambisa dake jihar Borno yanzu haka suna taruwa  a dajin Suntai dake jihar Taraba, a cewar gwamnan jihar Darius Ishaku.
Ishaku ya bayyana haka a lokacin da babban Kwamandan soji mai kula da Runduna  ta 82 dake Enugu,Manjo Janaral Adamu Abubakar,  ya kawo masa  ziyara a Jalingo babban birnin jihar. 

Dajin na Suntai dai ya ratsa ta cikin kananan hukumomin Bali da Donga dake jihar da Kuma gandun dajin Gashaka /Gumti dake jihar. 

Ishaku ya nemi da a girke rundunar soji ta musamman a jihar domin fatattakar yan kungiyar ta Boko Haram da suke taruwa da kuma sauran bata gari da suke damun mazauna jihar.

Kwamandan rundunar yace yazo jihar ne domin nemo hanyar maganin matsalar rikicin manoma da makiyaya da kuma sauran matsalolin tsaro da suke addabar jihar.

Yayi kira da ayi tattaunawa da kuma samun hadin kai tsakanin jami’an tsaro domin kawo karshen matsalar tsaro da jihar ke fuskanta. 


Like it? Share with your friends!

0

You may also like