‘Yan Boko Haram Sun Kai Hari Kan Tawagar Motocin Gwamnan YobeDaraktan sashin tattara bayanai a hedkwatar tsaron kasar, Janaral Edward Buba ya yi bayanin cewar harin ya yi sanadin raunata jami’an tsaro shida kana daya ya riga mu gidan gaskiya.

Janar Buba ya ce harin, ya faru ne kilomita shida daga garin Benisheikh, akan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu, a lokacin Gwamnan jihar Yoben ba ya cikin tawagar, sai dai manyan mukarraban gwamnatinsa.

Ciki kuwa har da sakataren Gwamnatin, Baba Mallam Wali, mai bada shawara kan sha’anin tsaro, Janaral Dahiru Abdulsalam, mai bada shawara kan lamurran addinai, sai kuma motocin soji masu sulke biyu, da wasu kirar Hilux da ke girke, masu manyan bindigogi, motocin ‘yansanda da kuma na DSS.

Hedkwatar tsaron Najeriyar ta ce a take aka kai dauki daga Brigade na 29 dake sintiri akan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu wadanda suka taimaka wajen debo wadanda suka sami rauni da janyo motocin da aka lalata yayin harin.

A halin yanzu dai sojojin brigade na 29, karkashin jagorancin wani Janar, sun bazama cikin dajin don neman ‘yan ta’addar da suka tafka wannan danyen aiki, yayin kuma da jamio’an tsaron da suka sami rauni ke jinya a wani asibiti.

Wannan hari dai na nuna cewar har yanzu da sauran aiki wurin kokarin kawar da yan ta’addan da suka shafe shekaru sama da goma suna cin karensu babu babbaka, duk kuwa da ikirarin da mahukunta ke yi cewa sun kawo karshensu.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like