‘Yan Boko Haram Sun Kawo Cikas a Tattaunawarsu da Gwamnati


wp-1473924637932.jpg

 

A wani taron manema lanbarai, Ministan yada labarai da al’adun gargajiya Alhaji Lai Mohammed ya bayyana irin cikas din da gwamnatin tarayya ta samu a tattaunawar da ta ke da Kungiyar Boko haram game da kwato ‘yan matan Chibok 218 da yanzu haka ke hannunsu.

Ministan ya bayyana cewa sai da ana daf da da kammala tattaunawar, bayan an shafe makonni biyu ana yi, sai ‘yan bindigar suka sake shawara suka gindaya wasu sabbin sharudda, wadanda suka saba da wadanda gwamnatin ta yarda dasu a baya, wadanda kuma gwamnati bata iya gamsuwa da su ba.

Ya ce wannan al’amari shi ya haifar da cikas a batun sakin’yanmatan. Sai dai har yanzu suna nan suna kokarin shawo kan al’amarin yadda za su ci gaba da sulhun.

Tun a watan 7 na shekarar 2015 ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya baiwa jami’an tsaro umarnin su fara nemo hanyoyin ceto ‘yan matan Chibok, inda kokarinsu ya kai ga matsayin tattaunawar.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like