‘Yan Boko Haram Sun Yi Wa Mai Garin Talari Yankan Rago


boko-haram-attack-gombe

 

A safiyar jiya Litinin, ‘Yan kungiyar Boko Haram suka yi wa kauyen Talari kwantan bauna a yayin da ‘yan kauyen ke barci suka yi wa mai garin da dansa yankan rago.

Haka kuma sun kone gidan shi kurmus. a yayin da ‘yan garin suka fuskanci abunda ke faruwa sun yi yunkurin tserewa inda a nanma ‘yan kungiyar suka bude musu wuta, suka kashe mutane biyu , da dama kuma suka jikkata.

Wani jam’in kato da gora a jahar Borno Abbas Gava ya tabbatar da faruwar al’amarin ga manema labarai ta wayar tarho, inda ya bayyana cewa Talari kauye ne da ke tsakanin kauyukan kilakia da Chibok a karamar hukumar Damboa

 

A kwanakin bayan nan, ‘yan ta’addan sun karfafa hare hare a kauyukan kayau da ke kusa da Damboa da Chibok a jahar Borno wadanda suka hada iyaka da dajin Sambisa.

Yawancin wadannan hare hare ba su zuwa kunnen manema labarai a sakamakon yanayin kebewa da kauyukan ke da shi da kuma rashin jami’an tsaro da za su kai masu dauki cikin gaggawa.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like