Tun bayan sanarwar da kungiyar ISIS tayi na nada sabon shugaban Kungiyar Boko Haram dake gabashin Najeriya wato Abu Mus’ab Al-barnawi zaman lafiya ya kare a tsakanin ‘yan Kungiyar inda tsohon Shugaban Kungiyar Abubakar Shekau yake ikirarin har yanzu a shine shugaban Kungiyar kuma suna nan suna shirin Yakar kasashen Africa baki daya.
Wani sabon video ya nuna yaran sabon shugaban Kungiyar suna harbe-harbe da bindiga mai carbi, da kuma tayar da bama bamai akan yaran tsohon Shugaban Abubakar Shekau.
Koya zata kasance a tsakanin Kungiyar? Ku ci gaba da kasancewa damu da samun ci gaban labaran.