Yan Chinar Da Aka Ceto Daga Hanun Yan Bindiga Sun Fara Samun Kulawar Asibiti
Sojojin Najeriya sun kwato mutanen da aka sace ne a wani samame da suka kai karshen mako a jihar Kaduna da ke arewacin kasar.

Kakakin rundunar sojin saman Najeriya, Gabriel Gabkwet ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, inda ya ce an kubutar da ‘yan kasar China ne daga yankin Kanfani Doka da Gwaska da ke jihar Kaduna bayan wani farmaki da suka kai cikin dare.

Ya ce masu garkuwan sun yi watsi da wurin buyansu tare da wadanda suka sace da ma makamansu.

Ya ce an kwashe sama da watanni biyar suna hannun ‘yan ta’addan da suka yi garkuwa da su a wani wurin da ake hakar ma’adinai a karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja.

Gabkwet dai bai amsa kiran da Muryar Amurka ta yi masa nan take ba.

A wata sanarwa da gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello ya fitar a jiya Litinin, ya yabawa rundunar sojin sama bisa wannan nasarar da suka samu, ya kuma ce hukumomi za su ci gaba da hada kai da dukkan jami’an tsaro a jihar domin tabbatar da ‘yan kasa sun samu sukuni.

Jami’ai sun ce an kai ‘yan kasar China da aka ceto zuwa wani asibitin da ba a bayyana ba.

A harin da aka kai a watan Yuni a wurin hakar ma’adinan, an kashe jami’an tsaro akalla 22 da suka hada da ‘yan sanda da sojoji.

A ranar Litinin, kakakin karamar hukuma a yankin Kaura a jihar Kaduna ya shaidawa gidan talabijin na Channels da ke Legas cewa wasu ‘yan bindiga sun kashe akalla mutane 37 a wani harin da suka kai ranar Lahadi tare da kona gidaje sama da 100.

‘Yan sanda ba su ce uffan ba kan faruwar lamarin amma wani mai sharhi kan harkokin tsaro Chidi Omeje ya dora alhakin tashin hankalin a kan tserewar daruruwan fursunonin da aka yi a gidan yarin Abuja a watan Yuli.

“Lokacin da wannan batun gidan yari ya faru, kuma aka ce mana gomman ‘yan ta’adda da ake tsare da su sun tsere, a ina kuke ganin suka je? Ba a gaya mana cewa an sake kama su ba, don haka yanzu sun je sun sake farfado da ‘yan ta’addan. “

Sama da shekaru 13 ne Najeriya ta kwashe tana yaki da kungiyar Boko Haram da sauran kungiyoyin tada kayar baya a yankin arewa maso gabashin kasar. Kimanin mutane 300,000 ne aka kashe a rikicin.

Hukumomin kasar na kuma kokawa kan yadda za a shawo kan gungun masu satar mutane don neman kudin fansa da ke addabar sauran yankunan kasar.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like