‘Yan Fansho Na Bin Gwamnatin Kano Bashin Naira Biliyan 10 – Gwarzo


 

Shugaban hadaddiyar kungiyar ‘yan fansho, reshen Jihar Kano, Kwamaret Balarabe Gwarzo ya ce yanzu haka ‘yan fanshon jihar na bin gwamnatin Kano zunzurutun kudi kimanin biliyan goma.

Ya bayyana cewa suna bukatar a biya su hakkinsu domin rage radadi da zafin da yan fanshon ke ciki na rashin biya hakkokinsu a kan lokaci.

Ya fadi haka ne a taron ranar ‘yan fansho da aka gabatar a makon jiya a dakin taro na tunawa da marigayi Sani Abacha da ke unguwar Kofar Mata a Kano.

Haka kuma ya yi kira ga gwamnatin Kano a kan cewa a sayar da kadarorin ‘yan fansho a biya su hakkinsu tunda ba kyauta ba ne, hakkinsu ne da suka tara a lokacin da suke aiki na bautawa kasa, don haka ajiyar kadarar ‘yan fansho ba ta wani amfani ajiyeta.

Ya yi kira a yi gyara a kan kundin tsarin mulkin kungiyar ‘yan fansho na daukar kudi dai-dai a fanshon yan kungiya na banbanta sakataran gwamnatin da kuma karamin makaikacin ya ce tunda kudin akwai banbanci wajen yawa to ya kamata a banbance wajen daukar kudin shigar.

Shi kuwa a nashi bangaran, shugaban hukumar fansho ta Jihar Kano, Alhaji Sani Dawakin Gabasawa ya ce gwamnatin Kano na iya kokarinta na ganin an biya ‘yan fansho hakkinsu a kan lokaci illa wasu matsaloli na wasu hukumomin musamman bangaran malaman makaranta da ba sa biyan kasonsu na kudin fansho kamar yadda doka ta tanada, inda ya yi kira ga dukkanin hukumomi kowa ya rika ba da kason da doka ta ce ya bayar.

You may also like