‘Yan fashi, Masu Garkuwa Da Mutane Da Ƴan Ta’adda Na Neman Mallake Birnin Gwari


A yayin kiran da wasu mazauna yankin Birnin Gwari dake jihar Kaduna suka yi wa yan Jaridu ta waya a safiyar yau Talata, sun bukaci gwamnatin tarayya da ta jihar Kaduna da su kawo musu dauki a yankin ganin yadda barayi, ‘yan fashi da masu garkuwa da mutane suke cin karen su ba babbaka ba dare ba rana.

Mazauna yankin sun kara da cewa ko a safiyar yau an bada kudin fansa kimanin naira milyan biyar na wasu mutane da aka yi garkuwa da su a yankin. Sannan kuma a daidai lokacin hada wannan rahoto barayi sun tare tsakanin hanyar Birnin Gwari zuwa Funtua inda babu shiga babu fita.

You may also like