Yan fashi da makami, a ranar Alhamis sun dirarwa wani bankin kasuwanci dake Ifoki a karamar hukumar Ido-Osi ta jihar Ekiti.
Hakan na zuwa ne a yayin da kasarnan ke farfadowa daga alhinin mummunan fashin da ya faru garin Offa dake jihar Kwara inda aka kashe mutane da dama da kuma jami’an tsaro.
A ranar Alhamis mutane sun gudu domin tsira da ransu ya yin da yan fashin suka harbe ɗan sanda guda daya har lahira tare da jikkata wani abokin aikinsa.
Wani sheda da ya ganewa idonsa abin da yafaru ya ce yan fashin sun isa bankin da karfe hudu na yamma bayan da aka kammala hada-hadar kudi ta ranar.
Ya ce yan fashin sun rika harbi ba kakkautawa saboda sun gaza samun nasarar shiga harabar cikin bankin.
Amma kuma sun fasa wasu gilasai da aka yi ado dasu a gaban bankin tare da kuma lalata na’urar cirar kudi ta ATM. Kusan mintuna 30 suka shafe suna cin karensu babu babbaka.