Yan fashi sun kashe dan sanda guda da kuma wani ma’aikacin banki a jihar Ekiti


Yan fashi da makami sun dirarwa garin Ilawe-Ekiti dake karamar hukumar Ekiti ta yamma a jihar Ekiti ranar Talata inda suka kashe dan sanda daya da kuma ma’aikacin banki.

A cewar kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN harin na zuwa ne bayan makonni uku bayan da aka kai makamancinsa a bankin First Generation dake Ifaki Ekiti inda dan sanda daya ya rasa ransa.

Wasu ma’aikatan bankin da kuma wasu mutane aka rawaito sun jikkata a harin da ya dauki tsawon awa guda.

Wani da ya sheda abinda ya faru ya ce yan fashin sun dirarwa bankin dake kusa da fadar Alawe da misalin karfe 03:00 na rana inda suka aikata fashin ba tare da fuskantar wata turjiya ba.

An rawaito cewa yan fashin sun yi amfani da nakiya wajen tarwatsa kofofin bankin kafin su samu nasarar shiga ciki inda suka debe kudin da ba’a san yawansu ba.

Adebanji Alabi, Alawe na Ilawe-Ekiti ya tabbatar da faruwar fashin kana ya kuma bayyana kaduwarsa.

Basaraken gargajiyar ya koka kan yadda yan fashin suka mayar da yankin tamkar wani filin daga ta hanyar yin amfani da nakiyoyi.

You may also like