‘Yan Fashin Dajin Da Suka Sace Yara A Zamfara Sun Nemi Naira Miliyan 30
Rahotanni daga Najeriya na cewa, ‘yan fashin dajin da suka yi garkuwa da gomman yara a jihar Zamfara, sun nemi a biya su naira miliyan 30 kafin su sako yaran a cewar jaridar Daily Trust.

A karshen makon da ya gabata, ‘yan bindigar suka sace yara kanana da mata a wani kauye da ake kira Wanzamai a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Maharan har ila yau sun sace wasu gomman mutane a jihar Katsina da ke makwabtaka da Zamfarar.

Wasu mazauna yankin da jaridar Trust ta gana da su sun ce da farko ‘yan bindigar miliyan 60 suka nema, amma daga baya aka wanye akan miliyan 30.

Hukumomin tsaro yankin sun ce suna iya bakin kokarinsu don ganin sun kubutar da mutanen.

Wasu jihohin arewa maso yammacin Najeriya sun jima suna fama da matsalar masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa.

A ‘yan watannin baya matsalar ta lafa, amma a ‘yan kwanakin nan tana kara ta’azzara.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like