Wasu ‘yan fashin shanu a kananan hukumomin, Birnin Magaji,Maru da Gusau dake a jihar zamfara sun mika makamansu ga rundunar soji dake jihar.
Mai magana da yawun hukumar soji ta kasa, birgediya janar, sani usman ya shaidawa manema labarai haka yau a Abuja.
Usman yace makaman masu hatsarine kwarai dagaske, wadanda suka hada da bindiga samfurin G3 , da na gargajiya 434, dakuma kanana samfurin fistol 69.
An dai mika mkaman ne dai ga rundunar soji ta 233 bataliya ta daya, a idon makarraban gwamnatin jihar.