Yan gudun hijira 10,000 daga Kamaru sun kwarara zuwa jihar Benue


A ƙalla mutane 10,000 waɗanda suka yi gudun hijira daga ƙasar Kamaru yanzu haka sun samu mafaka a sansanoni da dama dake yankin Akwaya na ƙaramar Hukumar Kwande ta jihar Benue.

Shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jihar, Emmanuel Shior shine ya bayyana haka ga manema labarai a Makurdi inda ya jaddada cewa kwararan mutanen ya fara ciwa jihar tuwo a kwarya.

“Wani matsanancin hali ne da mutane suka shiga inda muke samun kwararar mutane zuwa ƙauyukan ƙaramar hukumar Kwande, mun tura tireloli  guda biyu  cike da kaya zuwa sansanoni biyu. Yanayin ba me kyawu bane  saboda babu hanyar mota zuwa gurin suna can cikin karamar hukumar Kwande ne.” Ya ce.

Shior ya lura cewa tuni aka ja hankalin gwamna Samuel Ortom kan halin da ake ciki tun makonni biyu da suka gabata inda shi kuma ya tuntubi  hukumar bada agajin gaggawa.

Shugaban hukumar wasu daga cikin mutanen da suka dawo yan kabilar Tiv ne dake zaune a Kamaru kafin rikicin ya barke.

You may also like