Majiyar sojojin Nigeria ta bayyana cewa yan gudun hijira kimani 3000 suka koma gidajen bayan a arewa maso gabacin jihar Borno bayan fatattakon mayakan boko haram daga yankin
Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto wani kakakin sojojin Nigeri Sani Usman yana fadar haka, ya kuma kara da cewa bayan bude manya manyan tituna guda biyu masu zuwa garin Damasak da kuma Baga daga birnin Maiduguri babban birnin Jihar, yan gudun hijira kimani 3000 ne suka yi amfani da wadannan tituna don komawa yankunansu.
Garin Damasak da ke arewa masu yammacin jihar ta Borno ta fada hannun mayakan Boko Haram ne tun shekara ta 2014. A cikin watan yulin wannan shekara mai karewa ne sojojin Nigeria suka fatattaki mayakan Boko Haram daga yankin.
A ranar Asabar da ta gabata ce shugaba Mohammadu Bohari ya bada sanarwan cewa sojojin kasar sun kwace iko da tungar Boko Haram mafi girma a kasar wato tunkar Sambisa.
Usman ya kara da cewa sojojin sun kafa shin gaye masu yawa a kan manya manyan tutunan da suke bude a wadannan yankunan na jihar Bornon Don tabbatar da cewa babu wani bara gurbi da zai saje da su ya wuce.
Mutanen fiye da dubu 17 ne suka rasa rayukansu tun lokacinda mayakan boko haram suka dauki makami a shekara ta 2009 sannan wasu kimani milion biyu suka kauracewa gidajensu