Yan Gudun Hijira 46,000 Ne Suka Dawo Jihar Borno A kalla mutane 46,000 da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu suka dawo birnin Maiduguri daga makotan kasashe a cewar hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA.

Shugaban hukumar Mustafa Maihaja wanda ya raba kayayyakin agaji ga mutanen a kananan hukumomin Bama da Banki dake Borno a ranar Asabar yace mutanen sun tsare ne zuwa kasashen Nijer, Kamaru da kuma Caji lokacin da ake tsaka da rikicin Boko Haram.

  Maihaja yace mutanen da yaki ya raba da muhallansu sun dawo gidane saboda nasarar da aka samu a yaki da ake da kungiyar Boko Haram. 

” Kusan mutane 46,000 akayi wa rijista a nan wurin,kuma muna karbarsu a kullin gwamnatin tarayya tana mai da hankali kan halin da rikici ya jefa mutane a yankin arewa maso gabas.

“Abinda muka saka a gaba shine mu basu kayan tallafi da suka hada da abinci da ma wanda ba abinci ba ga yan Najeriya da suka dawo daga kasar Kamaru,” Maihaja yace. 

Yace gwamnati tana sane da cewar tunda yanayin tsaro yayi kyau a yankin musamman ma a Borno, Mutanen da suka nemi mafaka a garuruwan kan iyaka na kasashen Kamaru, Nijer da Caji  zasu dawo gida. 

You may also like