Yan Gudun Hijira Sun Kai Hari Kan Ma’aikatan Agaji, Suka Kuma Lalata Motoci 5Mutane dake zaune a sansanin yan gudun hijira dake Maiduguri sun kai hari kan ma’aikatan agaji inda suka raunata wasu da dama.Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa yan gudun hijirar sun samu nasarar lalata motoci kirar jeep guda biyar.

Lamarin yafaru ne a sansanin yan gudun hijira na Gubio dake birnin.   Lokacin  da ake rabon kayan agaji da wata kungiyar bada agaji ta saba yi duk wata. 

Lokacin da mutanen suka fara rabon kayan agajin  sansanin yan gudun hijirar sun lura cewa kayan da ake basu bai kai yadda aka saba basu ba  inda suka ce yayi musu kadan. Shedun gani da ido sunce daganan sai suka fara jifan ma’aikatan agajin da duwatsu. 

Wani shedar gani da ido,Ali Umar, yace “yan gudun hijirar sun fara fadin bama so, kafin a lura da abinda yake faruwa tuni sun fara jifa da duwatsu inda suka lalata motoci biyar, sojojin dake aikin samar da tsaro a sansanin sunyi kokarin shawo kan lamarin amma abin yaci tura.

Wani dan gudun hijira dake zaune a sansanin, Bulama Gubio yace sun kasance ba tare da abinci ba na tsawon lokaci.

“Mun kasance cikin yunwa kusan wata biyu kenan babu wanda yazo ya bamu abinci da kuma su kazo sai suka rage yawan abincin mai makon kaso  uku da suka saba bawa kowanne iyali sai suka rika bada kaso biyu shine matan mu suka fara zanga-zanga yayin da yara kuma suka fara jifa ni kaina ban goyi bayan harin da aka kai ba,”Gubio yace. 

You may also like