‘Yan gudun hijira sun yi zanga-zangar yunwa a Maiduguri


 

 

Daruruwan ‘yan gudun hijira da ke cikin sansanoni da aka kafa a garin Maiduguri na jihar Borno a Najeriya ne suka gudanar da zanga-zanga a wannan alhamis inda suke nuna rashin jin dadinsu a game da rashin abinci da ruwan sha a inda aka tsugunar da su.

Masu zanga-zangar dai sun datse babbar hanyar da ta tashi daga Kano zuwa Maiduguri na tsawon lokaci, yayin da jami’an tsaro ke gefe domin tabbatar da doka da oda.

Wannan na zuwa ne a dai dai lokacin da hukumar UNICEF tace akalla mutane 49,000 ake saran zasu mutu a Arewa maso Gabashin Najeriya bana saboda karancin abinci mai gina jiki.

Sai dai jami’an hukumar NEMA sun ce suna da isashen abincin kula da yan gudun hijirar.

You may also like