‘Yan Gudun Hijiran Boko Haram Guda 5000 Ne Ke Dauke Da Cutar Kanjamau


 

Hukumomin kiwon lafiya na jahar Borno sun bayyana cewa, akalla ‘yan gudun hijiran da rikicin Boko Haram ya shafa guda dubu 5 ne ke dauke da cutar Kanjamau.

Wannan batu ya fito ne daga bakin wani babban jami’in yaki da cutar a jahar, Hassan Mustafa, wanda ya bayyana cewa, an samu wannan adadin ne a sansanoni uda g27 da ‘yan gudun hijirar ke samun mafaka.

Jami’in ya kuma ce, a kasarin masu dauke da cutar mata ne da aka ceto su daga hannun mayakan na Kungiyar Boko Haram.

Jami’in ya koka game da yadda ya ce cutar ta yi sanadiyar ajalin wasu daga cikin ‘yan gudun hijirar, al’amarin da ya danganta da rashin wayar musu da kai da kuma samun magunguna.

You may also like