Yan gudun hijirar dake jihar Adamawa  sun gudanar da zanga-zanga kan karancin abinci 


Daruruwan yan gudun hijira dake sansanonin Fufore da Malkohi a jihar Adamawa sun gudanar da zanga-zangar lumana kan karancin abinci a sansanonin na su.

Yan gudun hijirar da yawancinsu mata ne da kananan yara sun yi kira da shugaban kasa,Muhammad Buhari da ya sa hannu wajen maganin halin da suke ciki.

Jihar Adamawa na da sansanin yan gudun hijira biyu ne kacal da aka ware kuma Hukumar Bada Agajingajin Gaggawar Ta Kasar NEMA ce ke kula da sansanonin da ke kauyukan Fufore da Malkohi kuma suna dauke da yan gudun hijira 3000.

Yawancin yan gudun hijirar sun fito ne daga jihar Borno sun kuma shafe shekara biyu a sansanin suna jiran a mayar da su jihar da su ka fito.

A zantawar da su ka yi daban-daban da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN, yan gudun hijirar sun yi korafin cewa yawancin iyalin dake sansanonin suna rayuwa cikin mawuyacin hali saboda yunwa.

Mal Adamu Bukar daga sansanin Malkohi ya ce yana da mata daya da kuma yara uku kuma suna cin abinci sau daya ne kawai a rana.

“Tun farkon watan Janairu lokacin da suka bamu kayan abincin da suka saba bamu na wata, bamu sake karbar karin wani abu ba,”Bukar ya ce.

A cewar sa, mutanen da suke rayuwa a sansanin suna bukatar kayan abinci da gaggawa saboda kowane lokaci daga yanzu wasu mutane musamman yara kanana za su fara mutuwa saboda yunwa.

You may also like