‘Yan Gudun Hijirar Kamaru Sun roki Gwamnatin Kasar Da ta Maida su gidaDubban ‘yan Nijeriya da ke gudun hijira a makwafciyar kasar Kamaru sakamakon rikicin Boko Haram sun roki gwamnatin tarayya kan ta taimaka masu wajen dawowa da su gida Nijeriya.
Rahotanni sun nuna cewa akwai ‘yan gudun hijirar Nijeriya da ke Kamaru sun kai kimanin 80,709 kuma mafi yawansu ‘yan asalin jihar Borno ne.
 Da yake gabatar da wannan rokon, Mataimakin Shugaban ‘Yan gudun hijirar da ke Kamaru, Mista Asshigar Mohammed ya nuna cewa ba su fuskantar wata matsala dangane da Makaranta da harkar lafiya sai dai kawai suna kewar gidajensu da suka baro.

You may also like