Hukumar Kula da ‘Yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce ‘yan kasar Sudan ta kudu dubu 32,000 suka shiga kasar Sudan a cikin wannan shekara kawai, dan tserewa tashin hankali da kuma yunwar da ya dabaibaye kasar.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin kasar ta bayyana cewar mutane sama da 100,000 na fuskantar tsananin yunwa a kasar.
Hukumar kula da yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce hasashen ta na da, ya nuna mata cewar mutane 60,000 ake saran za su shiga Sudan a wannan shekara, amma adadin da aka samu yanzu haka ya nuna cewar ba haka abin yake ba.
Hukumar tace ana fargabar tabarbarewar al’amura wajen samun abincin da za’a ci a Sudan ta kudu ganin yadda tuni aka bayyana samun yunwa a kasar.
Sanarwar hukumar ta nuna cewar, wasu daga cikin yan gudun hijirar sun ce sun kwashe kwanaki 5 zuwa 7 suna takawa da kafafuwan su dan isa iyakar Sudan ta Jihar White Nile, kuma kasha 90 na bakin mata ne da yara kanana.
YHukumar tace yanzu haka yan sudan ta kudu 330,000 suka shiga Sudan tun fara yakin kasar.