‘Yan Indiya sun yi wure sanye da kayan kwallon Argentina da Faransa



India

Asalin hoton, ARUN CHANDRABOSE

Wadansu masoya kwallon kafa a jihar Kerala da ke kudancin Indiya sun burge mutane a kasar da kwallon kruket ke da matukar farin jini.

Auren Sachin R da matarsa R Athira ya fado ranar da za a buga wasan karshe na gasar cin kofin duniya tsakanin Argentina da Faransa.

Bakinsu ya zo daya a kan komai game da aurensu, amma sun sha banban a bangaren kwallon kafa.

A yayin da Sachin ke matukar kaunar Lionel Messi na Argentina, ita kuwa Athira tana goyon bayan tawagar Faransa ne.



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like