‘Yan jam’iyyar PDP 7000 ne suka sauya sheka ya zuwa APC a jihar Yobe


A kalla mutane 7000  ne ya yan jam’iyar PDP suka sauya sheka ya zuwa jam’iyyar APC a karamar hukumar Potiskum dake jihar.

Mutanen da suka sauya shekar sun bayyana rikicin da yaki ci yaki cinyewa, rabuwar kai da kuma rashin alƙibla dake addabar jam’iyar PDP a jihar a matsayin dalilinsu na sauya shekar.

Jagoran masu sauya shekar, Alhaji Saleh Jauro,ya ce jam’iyar ta rarrabu gida-gida ga kuma banbance da baza su daidaitu ba ya yin da bangarorin jam’iyar biyu dake karamar hukumar suke barazanar tsayar da yan takarkaru daban-daban a zaben shekarar 2019.

Wani jigo a jam’iyar APC , Alhaji Ibrahim Bomai wanda ya taka rawa wajen sauya shekar mutanen ya ce APC a shirye take ta karbi karin mutane da za su yi aiki wajen samun nasararta, a shiyar B da kuma jihar Yobe baki daya.

You may also like