‘Yan Kasashen Waje Masu Saka Ido A Zabe Sun Fara Isowa Najeriya
SOKOTO, NIGERIA – Duk da yake wasu ‘yan kasa na ganin sanya ido ga zaben baya da tasiri wasu na ganin akwai amfani ga tsarin.

Zabubbukan da ake gudanarwa a kasashen duniya sukan janyo hankalin masu saka ido daga cikin gida da kasashen waje domin su ga yadda lamurran zaben suke gudana domin su sheda wa duniya.

Haka ma a Najeriya, duk da yake akwai sauran mako uku a fara zabe, yanzu haka masu saka ido daga kasashen ketare sun soma shiga lungu da sako na Jihohin kasar domin soma sa ido ga tsarin zaben kafin ainihin ranar zabe.

Masu saka ido karkashin inuwar kungiyar tarayyar Turai suna kan zagaye Jihohin Najeriya akan wannan aikin. Na zanta da ayarin da ke kan zagayen jihohin Sakkwato da Kebbi.

Mai saka ido Malda ta ce gwamnatin Najeriya ce ta gayyato su domin su sanya ido kan zabe karkashin inuwar kungiyar Tarayyar Turai, ta ce a wannan zaben zasu duba dukkannin tsare tsare kafin zabe, da lokacin zabe kamar yekuwar neman zabe, ranar zabe da ma bayan zabe in za a samu korafe korafe.

Daga baya, a cewarta, sukan rubuta rahoton duk abinda suka gani su tura wa hedikwatar su dake cikin Babban Birnin Tarayya Abuja.

Duba da cewa duk lokutan da ake zabubuka ana samun masu saka ido suna zagayawa, ra’ayin ’yan kasa akai ya sha bamban. Wasu na ganin yana da tasiri wasu kuwa na ganin baya da tasiri.

Masu lura da lamurran yau da kullum na ganin cewa aikin da suke yi na sa ido yana da tasiri sosai domin ko ba komai yakan kasance kamar gyara kayan ka a haujin mahukunta domin idan sun san ana kallon abin da suke yi yana da wuya su kaucewa bin ka’idar aiki.

Duk da haka Farfesa Bello Bada na ganin akwai yadda za a kara inganta aikin na su.

Yanzu dai masu saka idon na kungiyar Tarayyar Turai sun ce sai sun zagaye dukan mazabu da zasu yi aiki su hadu da masu ruwa da tsaki a mazabun kafin ranar zabe.

Saurari cikakken rahoto daga Muhammad Nasir:Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like