Sabuwar kasuwar da aka fara ginawa a garin Jalingo na jihar Taraba, wadda har yanzu ba’a gama ginawa ba tun lokacin tsohon gwamnan jihar Jolly Nyame, kasancewar kasuwar na bayan gari, an sami takaddama akan mallakar kasuwar tsakanin jalingo da karamar hukumar yorro.
Wannan umurni ne yasa ‘yan kasuwar komawa da cigaba da bude shaguna, sai dai ba’a kai ko’ina ba jami’an ‘yan sanda suka bayyana inda suka kori ‘yan kasuwar daga shagunan su, lamarin da ya jefa da mada cikin mawuyacin hali.
‘Yan kasuwar sun bayyana rashin jin dadinsu, domin a cewarsu kwamishina ne ya basu izinin shiga shagunan, daga baya kuma lamarin ya canza.
Yayin da ‘yan kasuwar ke ci gaba da kokawa, gwamnatin jihar ta ce bada izinin ta kwamishinan ya bada wannan umurni ba. Mr Anthony, sakataren gwamnatin jihar Taraba ya ce bada yawun gwamnatin jihar kwamishinan ya bada wannan umurni ba.