‘Yan kato da gora, da mafarauta na amfani da bindigogin gargajiya wajen yin sintiri
‘Yan kato da gora dake arewa maso gabashin Nageriya sun taka rawar gani wajen yaki da kungiyar Boko Haram.
Wadannan ‘yan kungiyar mazan su da matan sun taimakawa jamia’an tsaro domin kare al’ummar su kana sun samu nasarar kame dubban ‘yan kungiyar ta Boko Haram sun mika su su ga jamia’an tsaron kasar, haka kuma suna baiwa sojojin bayanai masu muhimmaci da suka iya agaza musu wajen yaki da kungiyar.
Wasu ma cewa suka yi ‘yan kungiyar ta Boko Haram sunfi shakkar ‘yan kato da gora fiye da sojojin kasar.
Sai dai kungiyar ta Boko Haram a ramuwar gayya inda tayi ta wa mutane da yawa kissa tare da kone kauyuka, kana suna gargadin mutane su daina hada kai da gwamnati.
Yanzu haka sojojin Najeriya da na hadin gwiwa daga kasashen makwabta sun karya lagon kugiyar ta Boko Haram