Wasu ‘yan kunar bakin wake har su biyar sun kai jerin hare hare a kauyen Garki Muna da kuma yankin Kaleri da ke Gwamge a cikin Maiduguri inda suka yi sanadiyyar mutuwar mutane uku.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Borno, Victor Isuku ya ce wasu mata uku dauke da bindigogi ne suka rika harbi a yayin da suke niyyar shiga Maiduguri ta shinge sojoji da ke kauyen Garki Muna inda bama baman da ke jikinsu ya tarwatse wanda ya hallaka wani dan kato da Gora.
Ya kara da cewa bayan awa uku da kai wannan hari sai kuma was mata ‘yan kunar bakin wake suka sake kai wani hari a yankin Kaleri inda mutum hudu suka rasa rayukansu wanda ya hada da ‘yan kunar bakin wajen su biyu.