Yan Kunar Bakin Wake Sun Kai Hari Jami’ar Maiduguri 


Yan kunar bakin wake sun kai hari a jami’ar Maiduguri,wannan dai shine hari na biyu da aka kaiwa jami’ar cikin wannan makon. 

Karar bom guda biyu ta girgiza harabar jami’ar a adaren jiya. 

Bom na farko ya fashe ne da misalin da misalin karfe 11 na dare yayin da wani dan kunar bakin waken ya sake tashin wani bom din da misalin karfe 12.

Shugaban daliban jami’ar Abu Hanifa Babati ya tabbatar da faruwar harin.

Yace harin farko “ya farune a sashen tsangayar karatun aikin likitan dabbobi, bayan da dan kunar bakin waken ya tada bom din”

Yace bom na biyu ya fashe ne a wajen dakin kwanan dalibai mata da ake kira BOT. 

Babati yace daliban jami’ar sun kadu matuka saboda fashewar bom din. 

Mai magana da yawun rundunar yan sanda ta jihar Borno Victor Isuku, ya tabbatar da faruwar kai harin akan jami’ar.

” A ranar 18/05/2017  da misalin karfe 11:50, yan kunar bakin wake uku maza dauke da bom a jikinsu,sun samu damar shiga harabar jami’ar Maiduguri “yace a wata sanarwa da yafitar.

” A kokarin su na shiga dakin kwanan dalibai mata, jami’an tsaro sun dakatar dasu, daya daga cikinsu yayi sauri ya tada bom din  dake jikinshi inda ya mutu nan take.

“Ragowar maharan sun tayar da bom dinsu a wani wuri da ake aikin gini a harabar jami’ar,inda suka kashe kansu su kadai.Jam’ian tsaron makarantar uku sun samu rauni a harin.”

Isuku yace tuni jami’an kwance bom na rundunar suka ziyarci wurin da bama-baman suka fashe. 

Harin na daren jiya na zuwa ne kwanaki biyar da Kai wani hari cikin jami’ar da yayi sanadiyar mutuwar jami’in tsaro  tare da raunata soja guda. 


Like it? Share with your friends!

0

You may also like