Yan Kunar Bakin Wake Uku Sun Kai Hari Birnin Maiduguri Yan kunar bakin wake uku a daren jiya juma’a sun tayar da bom a yankin Simari dake Maiduguri,babban birnin Jihar Borno, inda suka kashe kansu tare da raunata jami’an tsaron sakai da akafi sani da Civilian JTF su uku.

 Shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Borno, Satomi Ahmad, ya shaidawa jaridar The Cable,  cewa harin yafaru da misalin karfe 9:30 na dare. 

“ba a samu asarar rayuka ba, yan kunar bakin wake uku sune suka mutu , muna fata Allah ya cigaba da kare jihar mu” yace. 

” Abin bakin ciki, jami’an Civilian JTF sun samu raunuka, kuma tuni aka debesu zuwa asibiti inda suke karbar magani. ”

A yan kwanakin nan dai birnin Maiduguri na fama da rikici daga mayakan kungiyar Boko Haram, tun bayan da aka saki wasu kwamandodin kungiyar a musayar da akayi wacce takai ga sakin wasu daga cikin yan matan Chibok.

You may also like