Yan kungiyar Boko Haram Huɗu aka kashe a Borno 


Mutane huɗu da ake zargi da kasancewa yayan kungiyar Boko Haram ne aka kashe a wasu sababbin hare-hare biyu da suka faru a yankin arewaci da kuma na  tsakiyar jihar Borno.

Wasu yayan kungiyar da suka tsere suma sun rasa rayukansu a musayar wutar da sukayi da sojoji a karamar hukumar Gubio dake jihar yayin da wasu mata yan kunar bakin suka mutu bayan da bom din da suke dauke da shi ya tashi da su.

Mai magana da yawun rundunar soja ta takwas, Kanal Timothy Antigha a wata sanarwa da yafitar a ranar Lahadi ya ce sojoji sun kashe biyu daga cikin yan ta’adda da suke tserewa daga maboyarsu dake dajin Gambo- Yukku.

Ya ce babu sojan da ya jikkata ko kuma ya rasa ransa a harin.

Shima mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, Victor Isuku inda yake tabbatar da wani harin kunar bakin wake da rundunar ta dakile a cikin birnin Maiduguri.

Inda yace da misalin karfe 6:45 na yammacin ranar Lahadi wasu yan kunar bakin wake biyu suka yi yunkurin shiga birnin ta hanyar Mafa zuwa Dikwa.

Amma jami’an sintiri dake yankin ne suka hangosu domin gudun kada a kama su ne shine daya ta tayar da bom din dake jikinta inda suka mutu nan take.

You may also like