Yan Kungiyar Boko Haram Sun Kai Hari Birnin Maiduguri Tare Da Kona Gidaje Yan kungiyar Boko Haram sun mamaye wani yanki na birnin Maiduguri, suka rika harbin kan me uwa da wabi, tare da cinnawa gidaje wuta. 

Harin na zuwa ne kafin ziyarar da mukaddashin Shugaban kasa Yemi Osinbajo zai kai birnin a yau domin kaddamar da rabon hatsi a birnin Maiduguri. 

Shedun gani da ido sun ce yan kungiya dauke da makamai sun fara kai hari ta hanyar Damboa, inda suka kori mutanen dake unguwannin jiddari, Aridawari, Polo da kuma rukunin gidajen NNPC.

Dubban mutane ne suka kauracewa gidajensu saboda gujewa harbi da kuma yadda ake kona gidajen, da yawa daga mutanen sun gudune zuwa titin Baga dake tsakiyar birnin. 

Dukkanin mutanen da suke zaune a kauyukan da suka kewaye birnin sun bar gidajensu don gudun kada harin ya rutsa dasu. 

A sanarwar da rundunar yan sandan jihar ta fitar  tace “kowa ya kwantar da hankalinsa tare da zama a cikin gidansa,yansanda da jami’an Soja sun kara tura jami’an tsaro domin tunkarar maharan. “a saurari sauran bayani nan gaba kadan. 

A wata sanarwar da rundunar ta kara fitarwa “Boko Haram sun kai hari kan al’ummar jiddari Polo dake birnin Maiduguri,babban birnin jihar Borno, dake arewa maso gabashin Najeriya,mazauna yankin sun bar gidajensu tare da neman mafaka a al’ummomin da suke kusa dasu ,sojoji sun samu nasarar dakile kai harin  an jibge jami’an tsaro a yankin jiddari Polo,” a cewar sanarwar da mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya Sani Usman yafitar. 

You may also like