NAJERIYA‘Yan Kungiyar Niger Delta Avengers Guda 200 Sun Ajiye Makamansu a Jahar Imo 0 Gwamnan jahar Imo Rochas Okorocha ya karbi bakuncin ‘yan kungiyar tada kayar baya fiye da 200 daga kungiyar Niger Delta Avengers wadanda suka zo domin su ajiye makamansu ga gwamnan a gidan karbar baki na gwamnatin jahar. ‘Yan tada kayar bayan sun shafe lokaci mai tsaho suna tayar da hankali a yankin Ohaji/Egbema dake jahar. Gwamna ya yi kira ga sauran da su ajiye makamansu nan da sati daya, kuma ya ce gwamnatin na cikin tattaunawa da su. Yayin da yake jawabinsa, gwamnan ya ce: “ina nan ne domin na ceto ‘ya’yana yadda ‘yan sanda da sojoji ba za su ci gaba da harbe harbe ba, kuma ina nan ne domin na karbi sakon ku na isar da shi ga gwamnatin tarayya. Ina yi muku magana a matsayina na uba, kuma ina tabbatar maku da cewa za ku samu sabuwar karbuwa cikin al’umma.” Wasu daga cikin shugabannin ‘yan tada kayar bayan da suka halarci bikin sun hada Banga, Bobby Uzoma wanda a ke wa lakani da ‘commander general’ da Modestus Gift wanda a ke wa lakani da ‘No mercy Previous PostPreviousNext PostNext
Kungiyar Tuntubar Arewa Ta ACF Ta Tattauna Kan Batutuwan Tsaro, Yajin Aiki, Da Ambaliyar Ruwa by admin 6 months ago6 months ago
Kwamitin Hafsan Hafsoshin Najeriya Ya Ceto Dukkan Fasinjojin jirgin Kasan Kaduna Da Aka Yi Garkuwa Dasu by admin 6 months ago6 months ago
ASUU Ta Caccaki Ngige Kan Rijistar Sabbin Kungiyoyi Da Za Su Maye Gurbinta by admin 6 months ago6 months ago
Hukumar Kula Da Ayyukan ‘Yan Sandan Najeriya Ta Kori Wasu Manyan ‘Yan Sanda Bakwai, Ta Rage Mukaman Wasu by admin 6 months ago6 months ago
Yau, Ranar Malamai Ta Duniya, An Bayyana Muhimmancinsu Ga Cigaban Dan Adam by admin 6 months ago6 months ago
Cin Zarafin Mata Ta Hanyar Lalata A Jami’o’i Abin Tada Hankali Ne: Buhari by admin 6 months ago6 months ago