‘Yan Liverpool 12 ne za su buga wa tawagoginsu wasa



Mohamed Salah

Asalin hoton, Getty Images

‘Yan wasan Liverpool 12 ne aka gayyata tawagoginsu, domin buga wasanni a makon nan da na gobe.

A cikin makon nan za a buga wasannin neman shiga gasar kofin nahiyar Turai, Euro 2024 da ta Afirka da wasannin sada zumunta.

‘Yan wasan Liverpool da aka gayyata sun hada da Virgil van Dijk da Cody Gakpo da Ibrahima Konate da Andy Robertson da kyaftin Jordan Henderson.

Sauran sun hada da Diogo Jota da Kostas Tsimikas da Caoimhin Kelleher da Mohamed Salah da Naby Keita da Harvey Elliott da kuma Curtis Jones.



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like