Yan Majalisar Dokokin Jihar Kano 32 Sun Saka Hannu kan Takardar Neman  Tsige kakakin Majalisar 


Mambobin majalisar dokokin jihar Kano 32 ne suka sanya hannu a takardar neman tsige shugaban majalisar, Kabiru Alhasan Rurum 

 Yan majalisar na zargin Rurum da laifin yin kwana da kudi har naira miliyan 100 da ake zargin Aliko Dangote, ya bawa yan majalisar kan su dakatar da binciken da sukeyi akan Sarkin Kano Muhammad sunusi II. 

A ranar Talata kakakin Majalisar ya musalta zargin inda yayi barazanar gurfanar da Jaridar Daily Nigerian a gaban kotu, wacce itace ta fara bada labarin zargin cin hanci. 

Amma a wannan karon a bayanan da jaridar ta Daily Nigerian ta samu na nuni da cewa kakakin ya rabawa mambobin majalisar naira miliyan 2 kafin ya tafi kasar saudiya aikin Umara. 

Jaridar ta Daily Nigerian ta rawaito cewa kakakin majalisar yayi wani taro da shugabannin majalisar a Otal din Hilton dake birnin Makka, inda ya basu hakuri. 

 Amma bulaliyar majalisar Labaran Abdul Madari ya tsaya kai da fata sai shugaban ya sauka domin kare mutuncin majalisar. 

Mambobin da suke kan gaba wajen tsige kakakin majalisar sun ce  yan majalisar da suka sa hannun tsige kakakin sun karu daga 17 zuwa 32. 

 ” Mun tattara sa hannun yan majalisar da yawa don aiwatar da kudurinmu,laifukan kakakin majalisar suna da yawa, bawai kawai kudin da Dangote ya bayar ba ne kadai .Kawai mun gaji da irin laifukan da yake aikatawa, ” a cewar wani dan majalisar da ya nemi a boye sunansa

Majalisar dai zata cigaba da zamanta a ranar 7 ga watan Yuli. 

You may also like