‘Yan Majalisar Dokokin Jihar Kano Sun Shirya Tsige Kakakinsu


Yan majalisar dokokin jihar Kano sun shirya tsaf domin tsige kakakin majalisar, Alhaji Yusuf Abdullahi Ata.

Wata majiya mai tushe dake majalisar ta shedawa jaridar Daily Trust cewa ya zuwa daren jiya yan majalisa 21 ne suka sanya hannu a takardar neman tsige shugaban.

Majiyar ta ce tuni aka tsige shugabannin majalisar biyo bayan samun sahannun wakilai 21 da ake bukata domin tsige su.

Da aka tambayi majiyar ko me yasa yan majalisar suke son tsige shuwagabannin majalisar, majiyar ta ce “Dalilan suna da yawa amma babban a cikinsu shine na rashin iya gudanar da aiki,”

Majiyar ta kara da cewa karkashin shugabancin kakakin, majalisar bata fara zamanta sai karfe biyu na rana.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like