Yan Majalisar Tarayya Biyu Yayan Jam’iyar PDP Sun Sauya Sheka Zuwa APC


Wasu yan majalisar wakilai biyu da suka fito daga jam’iyar PDP sun sauya sheka zuwa jam’iyar APC.

Yan majalisar su ne Zachariah Jisalo mai wakiltar mazabar birnin tarayya Abuja,da kuma wakili Ahmad Tijjani daga jihar Kogi. Yan majalisar sun bayyana sauya shekar tasu a zaman majalisar na yau ta wasiku biyu da aka karanta a yau.

Yan majalisar sun bayyana cewa jam’iyyar PDP a jihohinsu na fama da rikici.

Amma kuma yayan jam’iyar PDP karkashin mai tsawatarwa marasa rinjaye, Yakubu Barde da kuma Ossai Nicholas Ossai, sun nemi majalisar ta bayyana kujerun mutanen a matsayin kujerun da basu da wakilai.

Amma kuma shugaban majalisar Yakubu Dogara yace tsarin mulkin kasa bai bayyana Irin rikicin da za a iya bayyana shi a matsayin rabuwar kai a jami’ya saboda haka sauya shekar tasu na cikin ka’ida.

You may also like