
Asalin hoton, Getty Images
Manchester United za ta kara da Barcelona domin buga wasan cike gurbin shiga Europa League zagayen ‘yan 16 da za su ci gaba da buga wasannin.
Karo na 14 da za a kara tsakanin Barcelona da Manchester United, inda kungiyar Sifaniya ta ci shida da canjaras hudu, yayin da ta Ingila ta yi nasara a uku.
To sai dai ‘yan wasan Manchester uku wato Antony da Anthony Martial da kuma Scott McTominay ba za su buga karawar ba.
‘Yan wasan ba su yi atisaye ba da Manchester United a safiyar Laraba, bayan da suke jinya.
Lisandro Martinez da wanda ke buga wasanni aro Marcel Sabitzer ba za su buga fafatawar ba, sakamakon hukuncin dakatarwa.
Sai dai Casemiro yana da damar buga karawar, wanda ke hukuncin dakatarrwa fafatawa uku, bayan jan kati da aka yi a masa a Premier League.
An bai wa dan wasan Brazil jan kati a karawar da United ta ci Crystal Palace a babbar gasar tamaula ta Ingila.
Ten Hag ya ce karawar tana da mahimmaci a kokarin da yake na kawo kamfar lashe kofin da United ke fama tun bayan da Jose Mourinho ya ci Europa League.
United ce kadai a Ingila take buga kofi hudu a bana, wadda za ta buga wasan karshe da Newcastle United a Carabao Cup.
Haka kuma kungiyar tana cikin FA Cup da Premier League da kuma Europa.